Spread the love

Shugabannin gudanarwar jam’iyar APC na kasa a hukumance sun sanar da reshen jam’iyar na jihar Ebonyi kan shirin da gwamna David Umahi ke yi na shiga jam’iyar. 

Shugaban jam’iyar APC  na jihar Hon. Eze Nwachukwu ne ya tsegunta labarin ga manema labarai. 

Nwachukwu ya ce  za a sanar da komawar a Abuja.

Labarin ya fito ne awa 24 bayan gwamnan ya gana da shugabannin jam’iyar PDP a sakatariyar kasa dake Abuja. 

Shugaban jam’iyar PDP ya halarci ganawar da ake ganin yunkuri ne na baiwa gwamnan hankuri kar ya bar jam’iyar. 

Ana sa ran gwamnan zai dawo jihar cikin satin nan don shirye shirye karbarsa a hukumance. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *