Spread the love


Masu garkuwa da mutane sun sace mai baiwa gwamnan jihar Sakkwato Allhaji Aminu Waziri Tambuwal  shawara kan aiyukka namusamman Honarabul Sa’idu Muhammad Gumburawa tsohon danmajalisar tarayya da ya wakilci kananan hukumomin Kware da Wamakko.

Masu garkuwar sun tafi da Sa’idu Gumburawa ne da  misalin karfe biyu na daren Litinin cikin ruwan sanyi ba wata hatsaniya  a garin Gumburawa dake cikin karamar hukumar Wamakko.

Masu garkuwan sun zo ne saman babura kusan su 11 suka tsalka gina gidansa a baya da nufin su tafi da daya daga cikin diyansa kuma sun dauko wanda suka so tafiya da shi uwar yaron ta hana a tafi da shi, sai hatsaniya ta kaure a tsakaninsu abin da ya sanya uban yaron ya fito ya kuma roke su da su tafi da shi su bar yaron, haka an kayi sun tafi da shi ba wata rigima.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Sakkwato ASP Muhammad A. Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce a jiya Litinin da misalin  karfe 3:30 na dare aka sanar da jami’ansu dake karamar hukumar Wamakko an sace Honarbul Sa’idu Gumburawa da misalin karfe 3:00.

Ya ce jami’ansu sun zagaye ko’ina anan take sai dai ba su hadu da mutanen ba har zuwa lokacin da aka tattauna da shi babu wani labari da aka samu kan lamarin ba su samu wani bayani daga danginsa kan ko mutanen sun kira kan abin da suke so a bayar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *