Tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya dauki nauyin karatun matasa 45 ‘yan asalin jihar Sakkwato a Lead city dake Ibadan jihar Oyo domin karatun digiri na daya.

Matasan za su karanci kwasa-kwasan injiniyanci da likitanci domin kara bunkasa haujin ilmi a jihar Sakkwato.

Sanata Wamakko a lokacin da yake baiwa daliban takardun gurabun karatun da suka samu ya roke su da su mayar da hankali a wurin karatunsu kar su yi wani abu da zai kawowa karatun cikas, haka ma kar su yi wasa da wannan damar da Allah y aba su ta hanyarsa.

Ya yi kira gare su kar su yi duk wani abu da zai  kawar da  martabar danginsu da  jihar Sakkwato, ya ce ilmi ne mafi kima da za ka baiwa mutum a rayuwa.

“Makudan kudin da aka kashe na ganin kun samu wannan damar kar ku yi wasa da ita ku zama jekadu nigari.

“Ku tabbata ba ku shiga cikin kungiyoyin irin na asiri da wasu da za su bata tarbiyarku ba, don gudun dana sani a cikin rayuwa” Wamakko ya shawarce daliban 

Bayan daliban da za su karanci Injiniya da Likitanci akwai masu karatun sanin  makamar aikin gwamnati da sadarwa da Kimiya da Sanin halayyar dan adam, da sauransu. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *