Spread the love

Babbar kotun jihar Kaduna dake zamanta a garin Zariya ta watsi da bukatar hana nadin sarkin Zazzau Alhaji Nuhu Bamalli da gwamna jihar Nasir El-rufa’i da aka shirya yi a ranar Litinin mai zuwa 9 ga watan Nuwamba.

Lauyan mai kara Ustaz Yanus(SAN) ya sanya bukata gaban kotu ta hana nada kowa a matsayin sabon sarkin Zazzau har sai kotu ta saurari korafe-korafe da suka shigar kan nadin Sarkin Zazzau da gwamnatin Kaduna ta yi.

Mai Shari’a Alkali Kabiru Dabo ya ce yanda muhimmanci sarakuna suke a cikin al’umma ana iya samun hargitsi in aka aminta da bukatar hana nadin sarautar wanda gwamna ya nada saboda korafe-korafen da akwai kansa.

Alhaji Aminu Muhammad Bashar Iyan Zazzau shi ne yakai gwamnatin Kaduna da sarkin Zazzau da masu zabar sarki su biyar Kotu don yana kalubalantar nadin sabon sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *