Spread the love


Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal.

Shugaban hukumar zakka da wakafi na jijar Sakkwato ya ce akawai bukatar masu hali su rika taimakawa sha’anin lafiya ba wai a saki komai ga gwamnati ba, bayar da taimakon magani ko wani abu da maras lafiya ke bukata.Shugaban ya yi wannan bayanin a ofishin hukumar dake birnin Sakkwato lokacin rabon kudin magani da hukumar ke yi lokaci-lokaci, da kuma magunguna da Murtala Dan’iyan Jarma ya bayar a rabawa mabukata. 


Idan za a  iya tunawa  a watannin baya dan kasuwar ya ba da   tallafin magunguna wadanda aka raba ga wasu Asibitoci da ke jihar, a yau hukumar ta isa raba sauran.

Sadaukin Sakkwato ya yabama dan kasuwar akan wannan tallafin da ya bayar ya ce “Yanzu haka magungunan da dan kasuwar ya bayar a watannin baya basu  kare ba a wasu asibitoci”


   Ya yi kira ga ‘yan kasuwar dake jihar da su yi hubbasa wajen tallafawa al’ummar da suke cikin wani hali  kana su yi koyi da wannan tilon da ke baiwa Hukumar tallafin maganin dan rabawa.


 “Ko  ba a kawo  ga hukumar Zakka ba, kowa ya duba dan uwansa ko makwabcinsa da baida lafiya Sai ya taimaka masa ko ya kai Asibiti” a cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *