Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Gwamnan jihar Sakkwato ya aza harsashen ginin kamfanin takin zamani da zai lakume kudi dala Amerika miliyan 13 kusan naira biliyan biyar Kenan, wanda kamfanin takin zamani na OCP Afirika zai samar a unguwar masana’antu dake Kalambaina a jihar Sakkwato.

A cewar Gwamnan Kamfanin zai iya samar da ton dubu 200 a shekara, abin da zai iya bunkasa harkokin kasuwanci a jihar da kashi 100, gwamnati za ta rika sayen kayan kamfanin a kalla sau daya a shekara, za a kamala tare da soma aiki a watan Juli sabuwar shekara mai zuwa.

A kan wannan aikin gwamnatin jiha ta baiwa kamfanin fili mai fadin hekta 10 tare da takardar mallaka ta gwamnati cikin awa 24 aka mika masu takardar C of O a shekarar data gabata.

Tambuwal ya ce gwamnatinsa ba ta wasa ga abin da zai ciyar da jihar Sakkwato gaba a kowane bangare, balle ga abin da zai kara habaka noma don samar da canjin da ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *