Spread the love


Malamin addinin musulunci Shaikh Abduljabar Nasiru Kabara a hirarsa da kafar yada labarai ta BBC ya ce binciken da ya yi ya tabbatar masa kashi 75 shi’a tafi sunnah gaskiya kan riginginmu da ake yi yanzu.

Ya ce “ka ce min dan sunnah a yanzu shi ne damuwata yafi damuna ma’ana Ahalul Sunnah ba sunnah ba ahalul sunnah.”


Shaikh ya ce zuwa yanzu ba wani malami da ya yi min   bayani a bayanan dana nema. “an ce bangane abu ba  kuma an kasa wanda zai ganar dani,  a ganina kare addini nike gina shi nake, duk malamin da ka ji ya ce ina rusa addini a’a ina rusa abincinsa ne, amma ba addini nake rusawa ba Allah ya tsare ni”.

Ya ce duk wanda ya ce min shi’a ka ke yi zan tambaye shi miye shi’a a wurinka amsar da ya bani da ita zan ba shi amsa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *