Spread the love


‘Yan sanda a jihar Kano sun kama tare da  gabatar da Fahad Ali gaban kotun Majistere dake sansanin Alhazai kan zargin ya yi garkuwa da ‘yarsa mai shekarru hudu ya kuma nemi fansar miliyan 2 wurin Matarsa kuma ita ce mahaifiyar yarinyar. 

Mai gabatar da karar ya fadawa kotu cewa Shamsiyya Mohammad mahaifiyar yarinyar ce ta kawo maganar a ofishin ‘yan sanda an yi garkuwa da ‘yarta har an kirata a waya da cewa in ba ta bayar da miliyan 2 kudin fansa ba  Za a kashe yarta.

Bayan sati biyu ana bincike ‘yan sanda suka gano Fahad mahaifin yarinyar ne ya rika kiran waya kuma aka same shi da yarinyar da ya yi garkuwa da ita. 

Mahaifin yarinyar bai yarda da laifinsa ba bayan an karanta masa gaban kotu. 

Alkalanyar kotu   Sakina Aminu,  ta ba da umarnin a tsare wanda ake zargi a kurkuku har sai 24 ga wannan watan domin cigaba da sauraren kara. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *