Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano


Wasu gungun ‘yan daba a unguwar Sani Mainagge dake cikin birnin Kano a karamar hukumar Gwale sun kashe wani matashi mai suna Auwalu Halilu a yunkurinsu na yi masa kwace bayan ya taso daga mauludin Annabi Muhammad S. A. W.


Majiyar Kano Focus ta ruwaito al’amarin ya faru ne a daren ranar Lahadi ya yin da ake tsaka da yin Mauludi a yankin garin.


Majiyar ta  ce ‘yandaban na fakewa ne a cikin makabartar Gwale su kuma tare dukkanin wanda ya taso daga wurin mauludi ko kuma zai wuce ya tafi harkarsa su yi masa kwace.


A cewar Muhammad Shehu ‘yan daban sun tare Auwalu Halilu ne cikin dare da nufin yi masa kwace, suka kuma soke shi da hakan ya yi sanadiyyar ransa.


Ya ce tun da aka fara mauludi ‘yan daban ke fakewa cikin taron masu mauludin sun aikata ta’asarsu.


Wannan lamarin akwai bukatar gwamnati da jami’an tsaro a jihar su tashi tsaye domin magance lamarin
Malam Shehu ya ce ‘yan daban sun mamaye unguwar ne ta Sani Mainagge a daren Lahadin da misalin karfe biyu na dare har zuwa karfe uku suna cin karensu ba babbaka.


Margayin ya samu tsagewar kashi sakamakon saran da ‘yan daban suka yi masa.


Sa’idu Ahmad dan uwa ne ga marigayin, ya ce ayyukan ‘yan daban ya dade yana addabarsu a unguwar, a cewarsa wani lokacin ma har gidajen jama’a suke shiga.
“Munyi iya yin mu amma abin yaci tura muna kira da a dauki mataki.


Anata bagaren mahaifiyar mamacin, Naja’atu Musa Sheka tayi kira ga mahukunta dasu kwato mata hakkin danta.
A cewarta an kashe danta ne ba bisa laifin komai ba, bayan da aka sari  yaron nata sun sanar da hukumar ‘yan sanda.

Ta ce  za su zuba ido su ga hukuncin da jami’an tsaro za su dauka wajen nemo hakkin danta domin akwai bukatar gyara lamarin a kare sauran yaransu da suke raye. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *