Spread the love

Malam Murtala Bello Assada ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sarkin musulmi Sa’ad Abubakar kan kin magana da suka yi a batancin da aka yi wa manzon Allah wanda shugaban kasar Faransa ya yi, ya nuna hakan bai dace ba yakamata su nuna addininisu da Manzon Allah yafi masu komai a duniya.

Malamin ya ce son duniya da tsoron mutuwa kawai zai sa a ci zarafin manzon Allah musulmai su kama bakinsu gudun su yi magana a daina basu kashin miya.

Ya ce a tsarin addinin musulunci duk wanda ya zagi Manzon Allah Muhammad S. A. W kashe shi ake yi, don haka yake kira ga musulmai su kauracewa kayan Faransa domin karya tattalin arzikinta.

Malamin a wurin da yake gabatar da karatu ya yi kira da malamai su fito su yi magana kan lamarin, suma gwamnoni musulmai da sarakuna su ce wani abu kan lamarin in dai har manzon Allah ya fi masu komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *