Spread the love


Hukumar gudanarwan kamfanin Kaduna electric, na sanarda abokan kasuwanci cewa daga yau lahadi 1, ga watan Numamba, 2020, ta aiwatar da sabon jadawalin biyan kudin wuta da ya fara aiki a yau wanda aka canza.

Shugaban Sashen Sadarwa na kamfanin Abdulazeez Abdullahi ne ya sanya hannu a sanarwar da Managarciya ta samu ya ce abokan kasuwanci masu amfani da Mita na zamani wato( prepaid meters) su ne za su samu ganin sabon jadawalin a yau Lahadi,1, ga watan Numamba 2020, a katin da suka saya. 

Sa’annan abokan kasuwanci masu bill wato post-paid za su ga canjin sabon jadawalin a bill dinsu da zai fito na watan Numamba.


Shugaban ya ce sabon jadawalin kudin wuta da aka amince kuma a ka tabbatar yashafi rukunin abokan hulda da su ke akan rukunin A, B da kuma C ne kawai. 


“Abokan hulda na rukunin A za su amfana da ragi na kashi goma wato 10% sai abokan hulda na rukunin B su kuma sun samu ragi na kashi goma da digo biyar wato10.5% sai kuma wadanda suke rukunin C za su amfana da ragi na kashi talatin da daya  31%. 


“Sabon jadawalin bai shafi abokan hulda da su ke rukunin D da kuma E ba.” a cewarsa.


Ya ce Kamfanin Kaduna electric ta jaddada kudurinsa wajan ganin ya samar wa abokan kasuwancinsa na kowane rukunin na awowin hasken lantarki dakuma tabbacin samar da ingantatciya da wadatarciyar hasken wutan lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *