Spread the love

 

Kotun sauraren karar gwamnan jihar Edo ta soma zamanta domin fara sauraren korafin zaben Gwamna Goodwin Obaseki a karo na biyu da aka yi a 19 ga watan Satumba.

Godwin na jam’iyar PDP hukunar zabe ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe da tazara mai yawa. 

Jam’iyun da suka nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon zaben sun hada da; Action Democratic Party (ADP), Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Allied Peoples Movement (APM) and New Nigeria Peoples Party (NNPP).

A jawabinsa shugaban alkalan da za su saurari karar Alkali  Abdulrazaq Abdulkareem,  a ranar Jimu’a ya ce za su kammala korafen da aka gabatar musu guda biyar cikin lokaci.

Haka ma ya ce za su gudanar da aikinsu ba tare yin bangarancin kowace jam’iya ba. 

Za a ci gaba da sauraren karar 7 ga Disamban wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *