Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Katsina sun tabbatar da mutuwar mutum 17 ciki harda mambobin kungiyar sintiri da dan sanda daya a lokacin ‘yan bindiga suka kawo hari a kauyen Diskuru a karamar hukunar Dandume jihar Katsina. 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isah ya ce a harin da maharan suka kawo kan mai uwa da wabi nan take suka kashe mutum 12.

A satin da ya gabata Sun zo kauyen ba su sha da dadi ba kusan mutum uku aka kashe masu. 

Kan haka suka tafi suka sake shiri sun zo sun fi 200 saman babura kowanensu na rike da bindiga AK47 da babar bindiga mashin gan. 

Maharan Sun kashe mutane da dama sun kone gidaje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *