Spread the love

Lamari mai rikitarwa ya faru a cikin al’ummar Mabushi a Abuja a ranar Assabar in da dan sanda ya kashe abokon aikinsa in da ya ya harbe shi a gidan da suke gadi abin da ya yi sandin barinsa duniya.

Lamarin ya faru da misalin karfe 10 na safe, majiyar da ta ga yanda lamarin ya faru ta ce ana zargin jami’in tsaron a buge yake kafin lamarin ya faru, da ya fahimci ya kashe abokin aikinsa nan take ya harbe kansa ya bar duniya.

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda na Abuja ASP Mariam Yusuf ta ki aminta ce wani abu kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *