Spread the love


‘Yan sumogal suna cin karensu ba babbaka kan bodar fita Nijeriya zuwa kasar Benin a gefen jihar Ogun hakan ya faru ne bayan janye jami’an tsaro wanda hakan nada nasaba da rigimar zanga-zangar #ENDSARS. 

A tabikin wasu mutane da suka yi magana da Daly trust sun bayyana ‘yan sumogal sun samu dama tun ranar Talata a satin da ya gabata sun ta shigowa da shinkafa ta waje safe da marece. Hakan ya sanya farashin shinkafar ya fadi da kusan 8000.

Muhammed Munnir,  mai kasuwancin shinkafar a kasuwar a Lafenwa dake  Abeokuta, ya ce  buhun shinkafa  25kg ta waje ana sayar da shi   N17000-N18000 sabanin tsohon farashi   N25000-N26000.

Ba bude boda aka yi ba sai dai jami’an tsaron wurin ne ba su nan shi ne yasa Sumogal suka ta yin shige da fice ba tsangwama hakan ya sa farashin shinkafa ta waje ya sauka. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *