Spread the love

Muhammad M. Nasir 

Jagoran jam’iyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu ya karyata bayanan da ake furtawa cewa ya bar kasar Nijeriya bayan harbe harben masu zanga-zanga #ENDSARS a Lekki.

Ya nuna damuwarsa kan satar da aka rika yi ga muhimman abubuwan jihar  mallakar daidaikun mutane.

Ya yi magana da manema labarai a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu a gidan gwamnati dake Marina ya ce bai je ko’ina ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta. 

Ya nemi gwamna ya binciko wadanda suka kai hari ga kayan mutane. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *