Spread the love

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana zirga-zira da ya sanya a jihar Lagos ragewar zai fara daga gobe Assabar.

Sakataren yada labarai na gwamnan Akosile ne ya fitar da bayanin cewa hana fita na awa 24 da aka sanya an rage shi ya koma daga 6 na marece zuwa 8 na safe.

Gwamnatin jiha a ranar Talata ne ta sanya dokar biyo bayan ketare iyaka da masu zanga- zanagar SARS suka yi a wasu sassan jihar.

Gwamnan ya nuna cewa za su sassauta dokar domin mutane su samu abin da za su ci kasuwanci ya gudana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *