Spread the love

Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles ta samu koma baya a duniya in da a yanzu ba ta cikin manyan kungiyoyin wasan Kwallo na duniya guda 30.

A rahoton da hukumar shirya kwallon kafa na duniya FIFA ta fitar ya nuna Nijeriya dake mataki na 29 ta koma mataki na 32 a duniya gaba daya.

A yankin Afrika kuma Nijeriya ita ce a mataki na uku a baya in da a yanzu Aljeriya sun karbe matsayin.

Nijeriya ta rasa wannan matsayin ne bayan wasan sada zumunci da suka yi a tsakaninsu da Ajeriya da Tunisiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *