Spread the love

Mazauna garin Jos musamman na kananan hukumomin Jos ta Kudu da Arewa dake jihar Filato sun yi biyayya ga dokar hana fita a gida ta awa 24 da aka sanya a jiya Talata.

Manema labarai da suka zagaya a birnin sun samu ko’ina a rufe ba wani motsi na mutane ko ababen hawa kamar yadda gwamnatin jiha ta bukata.

Jami’an tsaro ne kawai ke sintiri domin tabbatar da abin doka kamar yadda aka shata.

Sanya dokar ya biyo bayan wata hatsaniya da aka samu tsakanin magoya bayan abar jami’an tsaron SARS da wadan da ba su goyon bayan barin.

Mutanen birnin a jiya Talata sun ga yanda aka tarwatse kayan gwamnati aka kone wasu motoci da ba su ji ba su gani ba kan tarzomar.

Gwamnan jihar Bako Lalong bayan ga yanda lamarin ya rikide ne ya sanya dokar hana fita waje ta awa 24.

Gwamnan ya ce sun sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta kudu da ta Arewa daga 8 na dare har sai yanda hali ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *