Spread the love

Daga Muhammad Muhammad 

Ministan harkokin jinkai da bada agajin gaggawa ta Nijeriya Hajiya  Sadiya Umar Faruk ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shirya za ta rabawa mata dubu 150 tallafin kudi naira dubu 20 kowacensu domin su yi wani abu na dogaro da kansu in da rayuwarsu za ta canja radadin talaucinsu ya rage.

Minista ta yi wannan kalami ne a wurin kaddamar da kudin da rabon kayan wadan da ambaliya ya shafa a jihar Sakkwato ta ce dukkan wadan da za a baiwa kudin sai da aka tantance su kan haka gwamnatin tarayya da jiha za su yi aiki tare don tabbatar da an samu nasarar cimma manufar aikin.

Ta ce wannan yana cikin dimbin aiyukkan alheri na rage radadin fatara da gwamnatin Buhari ta samar don haka matan da suka ci gajiyar wannan tallafin su sanya kudin a hanyar da ta dace ta sana’a domin su iya dogara da kansu.

A bangaren tallafin kayan ambaliya ta zayyana abin da za a rabawa kanan hukumomin da za su ci gajiyar za a ba su siminti da kwano da katifa da Bargo da gidan sauro da kwanon rufi da shinkafa da masara da saurnsu.

Kowane magidanci a cikin wadan da za su ci gajiyar zai amfana da buhun siminti daya da bandur na kwano daya da karamin buhun shinkafa ko masara da gidan sauro daya da katifa da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *