Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya umurci sarakuna da uwayen kasa da kuma duk wani mai sarautar gargajiya dake cikin jihar ta Zamfara da su gudanar da addu’o’i na sati daya domin rokon Allah ya kawo muna karshen wannan matsalar ta rashin tsaro.

Matawalle ya bada wannan umurnin ne a lokacin da Sarakunan jihar a karkashin jagoran cin shugaban majalisar sarakunan zamfara sarkin Anka Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad sukaje fadar gwamnati, domin yi masa gaisuwar rasuwar shugaban jam’iyyar PDP na jiha, Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau, da kuma Sanata Alhaji Yusha’u Anka.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata takardar bayani wadda Sakataren yada labarai a fadar gwamnati Alhaji Jamilu Iliyasu Birnin-Magaji ya sa wa hannu kuma aka rabawa yan jarida a garin Gusau, babban birnir jihar Zamfara.

Bayanin ya kara da cewa Gwamna matawalle ya bada umurni ga dukkan masu sarautar gargajiya, da su tara limamai da manya manyan malamai domin su dukufa wajen yin addu’oi na musamman a masallatai da wurin wa’azi domin rokon Allah yayi muna maganin matsalar garkuwa da mutane, satar shanu, da dai sauran su, a duk fadin jihar Zamfara.

“A matsayin ku na shugaban nin al’umma kuma gaku kusa da su, to kunada yanda zakuyi ku taimaka wa wannan gwamnati bangaren hada kan jama’ar da kuke mulki da zimmar ci gaban wannan jihar tamu” inji matawalle.

Yace duk da irin nasarorin da suka samu ta hanyar kirkiro sulhu tsakanin jama’a da wannan gwamnati tayi, har wayau ana bukatar a koyaushe a rinka yin addu’oi domin rokon Allah ya kawar da duk wata matsala.

Gwamnan na Zamfara ya ce gwamnatinsa, na iya kokarinta na taga ta kawar da matsalar tsaro a duk fadin jihar.

Daga nan sai Matawalle yayi masu godiya ta musamman bisa ga irin goyon bayan da suke bashi wajen yada manufofi da shirye shiryen gwamnati, da kuma goyon bayan ganin cewa shirin sulhu da aka yi bai samu matsala ba.

Da yake jawabi Sarkin Anka, kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed yace sun kawo masa wannan ziyara ne domin suyi gaisuwar rashin da akayi na wasu muhimman mutane na jihar Zamfara watau, Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau da kuma Sanata Yushau Anka.

Sarkin Anka ya ce wayan nan mutane biyu sunyi rayuwa irin wadda ya kamata ayi koyi da ita, daga nan sai ya roki Allah da ya gafarta masu dukanin kura kuran su, hakama ya rokar wa iyalan su da ya basu hankurin jure ma wannan rashin da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *