Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A kokarin da ta ke yi na inganta ilmi, da maida martabar malaman makaranta, gwamnatin jihar Zamfara tace tayi karin girma ga malaman makaranta har su 6,000.

Shugaban ba da ilmi na bai daya, a jihar, Alhaji Abubakar Maradun, yayi wannan bayani yau litinin a fadar gwamnati dake Gusau, yayin kaddamar da shirin bada ilmin na bai daya don al’umma. Inda ya kara da cewa malamai a jihar Zamfara sun kwashe shekara goma babu karin girma.

Shugaban ya kara da cewa malamman makaranta sun samu wannan karin girma ne bisaga umurnin gwamna Bello Muhammed Matawalle, kuma duk an biyasu hakkokan su.

Maradun ya kara da cewa gwamnati ta gina tare da gyara Ajujuwa fiye da 1,000, kuma ta gyara ofis ofis da wurin kewaya wa daga shekarar 2019 zuwa yau a duk fadin jihar ta Zamfara.

“Lokacin da gwamna Matawalle ya hau karagar mulki a matsayin gwamna, yayi alkawarin bada fifiko ga harkar ilmi, har saida takai shelar sa dokar ta baci ga fannin ilmi.

“Matawalle ya nuna rashin jin dadin sa ga tabar barewar ilmi, inda aka samu yara da yawa wayanda suka bar karatu, a don haka ya jajir ce domin magance wannan matsalar.

“Wannan gwamnatin ta gaji bashin biliyoyin kudi na hada ka dab gwamnatin tarayya, inda gwamnatin data wuce ta bar masu wannan bashin” inji shi.

Ata bakin shugaban na bada ilimi na bai daya, wata ukku bayan da aka rantsar da gwamna Matawalle, ya bayar da kudin hada ka na shekarar 2017 da 2019, ga gwamnati tarayya.

“Cikin shekarar 2019, mun biya N2.5 biliyan na shekarar 2017 da kuma 2018, sannan mun samu taimakon N5.5 biliyan .

“Yanzu maganar da mukeyi mun biya namu kudin hada ka na shekara 2019 da 2020, Zamfara yanzu tana daya daga cikin jahohi hudu a duk fadin kasar nan da suka biya kudin hada ka na wannan shekarar.inji maradun.

Shugaban ya yi bayani cewa dan taimakon da suke samu ga gwamnatin tarayya ya taimaka kwarai wajen samun kayan koyar wa ga makarantun Furamare dana sakandare a duk fadin jihar Zamfara.

Daga karshe ya yabawa gwamna Muhammed matawalle bisa ga irin tunanin sa da kuma kasan cewar sa dan siyasa mai son cigaban ilmi and his a cikin jiha sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *