Spread the love

Manomin damina da rani da ya kwashe shekara 19 yana noma a karamar hukumar Rabah dake jihar Sakkwato Malam Nasiru Abubakar Rabah a zantawarsa da manema labarai a satin da ya gabata ya bayyana dalilin da ya sanya ya koma noman gyda a yanayin rani bayan lokacin damina  aka san ana aiwatar da noman.

“ni manomin  shinkafa, albasa da tafarnuwa ne, a shekarar da ta gabata na yi  tafarnuwa sai aka samu matsala ba ta yi kyau ba, ga fili nan ba a shuka komai ba ina ban ruwa ga banza kan haka ya sanya na yi tunanain shuka gyada haka aka yi gaskiya na samu alheri fiye da wanda nake samu a tafarnuwa,  na ga akwai amfani Sosai  in aka shuka gyada a noman rani, daga nan  na cigaba da yi.”

Kuna ganin in kun koma noman gyada gadan-gadan za ku iya sauya kasuwar gyada a Nijeriya?  Ya ce “In gwamnati ta shigo aka samu wayewar kai za a shigar da mutane da dama don a samu alheri, talakawa na cikin talauci yakamata gwamnati ta rika cika abin da take fadi in aka yi abin da ake fadi abinci sai an kai shi  wata kasa don sayarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *