Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Jam’iyyar APC a jihar zamfara tasha alwashin cin zaben cika gurbi na dan majalisar dokoki da zai wakilci karamar hukumar mulkin Bakura dake jihar Zamfara, wanda za’a gudanar ranar 31 ga wannan wata.

Da yake jawabi gaban dubban magoya bayan jam’iyyar a wajen kaddamar da kamfen yau Assabar a garin Bakura, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Alhaji Lawali M Liman Gabdon Kaura ya ce da yardar Allah dan takararsu, Alhaji Bello Dankande Gamji zai lashe wannan zaben bisa ga la’akari da irin yadda yayi suna a karamar hukumar mulkin Bakura.

Gabdon Kaura ya bayyana cewa Dankande mutumen mutane ne wanda ya ba da gudunmuwa mai yawa domin ci gaban Bakura da jihar zamfara.

“Ganin haka yasa nace indai wannan zaben ne to shi zaizo na daya, muna jiran lokaci ne kawai” inji shi.

Daganan sai yayi kira ga dubban magoya bayan su dasu kasance masu bin doka da oda lokacin gudanar da wannan zabe. ya kara dajan hankalin su da su guji yin duk abinda zai kawo rudani lokacin zabe.

Shugaban jam’iyyar ta APC, ya sheda masu da cewa lokacin zabe su yi koyi da maganar shugaban kasa Muhammadu Buhari na a jefa kuri’a a kasa a tsare a kuma raka har sai an gama kirga kuri’un su.

Anashi jawabi dan takarar kujerar dan majalisar jiha, wanda zai wakilci karamar hukumar mulkin Bakura, a karkashin tutar jam’iyyar APC Alhaji Bello Dankande Gamji kira yayi ga jami’an tsaro da su kasance a tsakiya kuma su bada tsaro yadda ya kamata a lokacin da kuma kammala zaben.

Dankande ya kara da cewa jam’iyyar APC ba za ta lamunta da yin almundahana kuri’u ba, lokacin wannan zaben na cika gurbi.

Ya kara da cewa, magoya bayan APC za su zama mutane masu kiyaye wa ga dokokin zabe, lokacin zaben, amma ya tabbatar da cewa ba za su bari a yi masu murdiya ba a lokacin jefa kuri’a.

“Daman mu masu bin doka da oda ne, kuma za mu bi duk dokar zabe sau da kafa, amma dai ba za mu yadda a sace muna kuri’u ba” inji Dankande.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *