Spread the love

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya aiyana Lahadi 18 ga watan Okotoba 2020 a matsayin 1 ga watan Rabi’ul Auwal 1442 watan Mauludi.

A takardar da shugaban kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai ya ce kwamitin cikin gida dana kasa sun samu labarin ganin wata kuma Sarkin musulmi ya aminta da sahihancin ganin. 

Wata na uku a tsarin kalandar nusulunci zai soma Lahadi bisa ga sahihancin fitar watan da aka samu. 

Watan Mauludi ya soma kenan hidima ta farinciki da taya ranar haihuwar Annabi Rahama za a yi ta yi har watan ya kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *