Spread the love

Matar gwamnan Sakkwato Hajiya Maryam Mairo Aminu Waziri Tambuwal a wurin bayar da tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa a wasu kananan hukumomin jihar Sakkwato ta tambayi al’ummar dake wurin tsakanin shugaban kasa Buhari da Gwamna Tambuwal wane ne yakamata a fara gode wa domin dukkansu sun bayar da tallafin ga mabukata.

“Mutane ko zaku taimakamin wa za a fara yiwa godiya shugaban kasa ko Matawalle?”

Mahalarta taron sun karba mata da a fara yiwa Matawalle, daga nan ta cigaba da jawabinta na godiya wanda shi ne za ta yi bayan raba kayan tallafin da aka gudanar a tashar Alu.

Ta ce ministoci sun kawo tallafi kan yanayin da ake ciki a kasa ana fama da talauci da rashin abinci suna godiya kwarai da tawagar da gwamnatin tarayya ta turo.

Ta godewa gwamna da hadin kan da ya bayar lamarin ya samu nasara.

Mairo ta yi kira ga wadanda aka daurawa nauyin rabon su yi adalci su rike amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *