Spread the love

Muhammad M. Nasir.

Jam’iyar adawa ta APC a jihar Zamfara a yau ta kaddamar da yaki neman zaben dan majalisar dokokin jihar da za a gudanar a 31 ga wannan watan.

Dubban magoya bayan jam’iyar ne suka yi sansani a babban filin taro na garin Bakura a cikin karamar hukumar Bakura dake jihar Zamfara.

Hankalin jama’a ya karkata ga zaben ne saboda wannan zaben shi  ne na farko da za a fara gudanarwa a jihar tun bayan da jam’iyar PDP ta dare saman kujerar mulki a jihar.

Jam’iyar PDP a baya adawa take yi a jihar kuma ba ta da wani dogon tasiri kafin daga baya kotun koli ta yanke hukuncin ba ta kujerun mulki a jihar saboda rikincin da APC ta samu kanta a tsakanin mambobinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *