Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Uwar gidan shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ta fitar da sakon a ceci jama’a a turakarta ta facebbok.

Aisha ta saka hotunan shugaban kasa tare da hafsoshin tsaron kasa, wakar mawaki Adam A. Zango na tashi wadda ya rera kan Arewa na neman daukin kan halin rashin tsaron da ta samu kanta ciki.

Uwar gidan shugaban kasa bayan wannan kalami ba ta ce uffan ba, abin da ta bari mutane su fassara iya fahimtarsu ga fitar da wannan magana a lokacin da ake ta zanga-zanga a kasa, wasu domin a kawo karshen cin zalin da ‘yan sanda ke yi a yankin Kudu wasu kuma saboda akawo karshen zubar da jini a Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *