Spread the love


 Kungiyar gwamnonin PDP karkashin jahorancin gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal sun nuna rashin gansuwarsu kan gwamnatin Muhammadu Buhari a dokar da ta samar na cire wani kaso a lalitar gwamnatin tarayya saboda aiyukkan asusun cigaban ‘yan sanda na kasa wanda Ahmad Aliyu yake sakataren zartarwar asusun. 

Kungiyar gwamnonin sun nemi shugaban kasa da majalisar tarayya su sake duba sashe na hudu da na daya cikin baka a cikin daftarin dokar 2019 da ya samar da asusun bunkasa aikin dan sanda wanda ya baiwa shugaban kasa damar cire kaso 0.5 daga lalitar gwamnatin tarayya a dukkan kudin da aka samu.


Gwamnonin sun ce ba da Kudin ga asusun ya sabawa doka saboda kudin Kasa na gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi ne kadai.


Kungiyar a jawabin da ta fitar bayan taron da suka gudanar sun ce duk wata kafa da za a baiwa kudi ba wadan nan ba yakamata a jingine ta. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *