Spread the love


Gungun ‘yan daba masu dauke da makamai sun farwa matasa masu zanga-zangar a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar Arewa.


Masu zanga zangar dai sun fito da karfe 9 na safe a jikin katangar Jami’ar Bayero da ke kabuga cikin birnin Kano,  bayan sun fara tafiya gungun ‘yan daba suka far masu da duka da sara da kwace, an raunata wasu masu zanga zangar ciki harda editan labarai na gidan radiyo B.U.K FM.


Bayan tarwatsewar masu zanga zangar ne jami’an tsaro suka zo suka kawo masu dauki inda suka tarwatsa ‘yan daban.


 Bayan  minti 30 masu zanga-zangar sun dawo sun tsaya a inda suke suna daga kwalaye da banoni da amsa suna da  rera taken samun tsaro a Arewa, na so jin ta bakin shugaban masu zanga zangar Aminu Sparo inda aka ce min ya bar gurin ba da dadewa ba.


Har zuwa karfe 11:30 dai masu zanga zangar suna   nan a wuri daya, yayin da aka jibge jami’an tsaro a gaba da bayan masu zanga zangar.


Zanga-zanga ana fatan ta samu nasara a cimma bukatar da ake nema na gwamnatin Nijeriya ta dauki matakin da yakamata a lokacin da ya dace. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *