Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya rantsar da Sabbin shugabannin hukumar zabe ta jiha bayan da majalisar dokoki ta aminta da nadin shugaba da mukarabansa da gwamnatin jiha ta aika mata domin tantancewa. 


Tambuwal a wurin rantsarwar da ta gudana a dakin taro na fadar gwamnatin jiha a Laraba data gabata ya ce shugaba da mambobinsa an zabo su ne bisa cancanta da kyakkyawar sheda da suke da ita kan aikin gwamnati  da suka yi.  


Ya yi kira gare su da su tafi su fitar da tsare-tsare da jadawalin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Sakkwato hakan zai baiwa gwamnatin jiha hasken yadda  za a gudanar da zaben nan ba da jimawa ba. 


Tambuwal a lokacin da yake taya su murna ya roke su da su rike gaskiyar da suke da ita wadda ita ta sanya aka zabo su kuma su yi wa Kowa adalci a lokacin da suke gudanar da aikinsu. 


Sabbin shugabannin sun hada da shugaba Alhaji Aliyu Suleiman da mambobi su biyar Mu’azu Garba Dundaye da Sidi Mukhtar Ibrahim, Umar Galadima Durbawa, Abubakar Haliru Dange da  Alhaji Musa Illela; dukansu za su zama mambobi na dindin a hukumar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *