Spread the love


Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya nada Sarkin Malaman jihar Sakkwato Malam Yahaya Muhammad Boyi.

Sannan kuma ya nada Malam Amadu Helele matsayin alkalin malamai na jihar. 

An gudanar da bukin nadin a gaban Sarkin musulmi cikin fadarsa a ranar Alhamis. 

Sarkin musulmi a takardar da ya aika masu ta tabbatar masu da sarautar ya ce an ba su mukaman ne don sadaukarwar su ga cigaban fada da al’ummar jihar Sakkwato. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *