Spread the love


Kodineta kungiyar masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya reshen jihar Sakkwato Kwamared Hussain Muhammad ya bayyana akwai kalubale a ayukkan yaki da cuta mai karya garkuwar jiki a sassan Arewacin Nijeriya. 


Yace  fiiye da Mutane Dubu Dari da Ukku, da Dari hudu da hudu (103, 404 ) ne ke kamuwa da Cuta mai Karya Garkuwar Jiki ta HIV a Najeriya Kowace Shekara bisa ga Kidiggar da akayi a 2019.

Ya fitar da kalaman ne a sakon bayanai da ya aikawa managarciya ya ce “A Jihar Sokoto, muna da sama da Mutane dubu Goma Shabiyu (12, 000 ) masu dauke da wannan Cutar dake karbar Magani, in da akwai karin wasu Daruruwan Mutane dake dauke da Cutar da basu sani ba, ko kuma sukaki amincewa da karbar Magani.


“Akwai kalubale daban daban wajen ayukkan yakar wannan Cutar a Sassan Arewacin Najeriya wanda Jihar Sakkwato na daga Cikin Jihohin dake fama da wannan Kalubalen.


“Daga Cikin Kalubalen da Jihohin Arewa ke fuskanta akwai Rashin Kulawar Gwabnatoci, AL’ADU, KYAMA da WARIYA akan Cutar da masu Dauke da Cutar.” a cewar kwamared. 


Ya kara da cewar Cutar ta HIV wacce cuta ce dake saurin yaduwa acikin Al’umma, tana kara yaduwa ne a Yankunan Arewacin Kasar nan, saboda yanayin da Yankin yake ciki a yanzu, wanda ya hada da Kariyar tattalin arziki, wanda ya haddasa yawaitar Talauci a Cikin Al’umma. A jihar Sakkwato har yanzu akwai Karancin wayar da kan al’umma akan Wannan Cutar da matakan Kariya akan ta.  hakan nada nasaba da rashin Samun Cikakkar Kulawar Gwamnati wajen Yakar Wannan Cutar a Juhar ta Sakkwato.


“A dukkan Jihohin Arewa maso Yamma dake Najeriya, a Jihar Sokoto ne kawai babu  Ofishin Hukumar Yaki da Cutar ta HIV wadda ake kira da SACA ( State Agency for Control of AIDS ) duk da cewa Jihar ta Sakkwato na daga Cikin Jihohin da suka yi dokar Kafa wannan Hukumar, amma yanzu haka bata da Ofishi nata na kanta mai zaman kan shi.


“Wannan Matsalar na daga Cikin Matsalolin da suka gurgunta Kokarin ayukkan Hukumomi masu zaman Kansu da Kungiyoyin da bana Gwamnati ba wajen rage yaduwar wannan Cutar a Jihar Sokoto.


“A Zaman da muka taba yi da Maigirma Gwamnan Jihar Sakkwato  Aminu Waziri Tambuwal, mun fahimci anniyar shi ta kara zare damtse wajen Yakar Wannan Cutar da Yaduwar ta a Jihar ta Sakkwato ta hanyar irin Karbar da yayi muna tare da bamu Kulawar da tace wajen Sauraron mu da kuma Korafe-Korafen da muka bayyana masa.


“Ba a Jihar Sokoto kadai ba, a Tarayyar Najeriya gaba daya an Shedi Kokarin Gwamna Aminu Waziri na Yakar wannan Cutar tare da samarwa masu dauke da cutar saukin rayuwa da kuma Gata, ta hanyar tabbatar da yin Dokar da zata basu Kariya a Lokacin da yake Kakakin Majalisar Dokokin tarayyar Najeriya           (Anti-Discrimination act 2014 ) wacce tuni ta zama doka da Shugaban Kasar Najeriya ya rattabawa Hannu.


“Duk da irin Wannan Kokarin na Maigirma Gwabna, a yanzu a wannan Jihar ta Sakkwato akwai gibi sosai daga Bangaren Gwamnati wajen Ayukkan Yakar Yaduwar Wannan Cutar, wanda muka kasa sanin inda Matsalar take.


Lalle akwai bukatar hankalin Gwamnati da Sauran Shugabannin Al’umma wajen bayar da Kulawar data dace akan yakar Yaduwar Wannan Cutar a Wannan Jihar.” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *