Spread the love


Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.

Matar Gwamnan Jihar Sakkwato Maryan Mairo Aminu Waziri Tambuwal wadda ita ce ta assasa gidauniyar MMAWT domin gudanar da lamurran jinkan jama’a da kare hakkin mata a cikin al’umma ta bayyana cewar gidauniyarta ta bayar da himma wajen share hawayen al’umma ta hanyoyi da dama.

Mairo Tambuwal ta bayyana cewar za ta ci-gaba da karfafawa al’umma, fadakar da su, tallafa masu a sha’anin kiyon lafiya, ilimi, sana’o’in da sauransu domin magance matsalolin da suke fuskanta.

“Gidauniyar MMAWT na kawar da matsalolin al’umma ta fuskar bunkasa ilimin ‘ya’ya mata, tallafawa a kiyon lafiya, rage cunkoso a Kurkuku, tsaftar muhalli, tallafawa zawarawa da kula da marayu da sauransu.”

“Shiraruwan Gidauniyata ba su da shinge, ba su da ko wace irin alaka da siyasa, addini ko kabila. Ba zan taba kaucewa manufar kafa wannan Gidauniyar ta inganta rayuwar al’umma ba. Rarraba wadannan kayan tallafin na da manufar rage radadin cutar Korona a wannan Jihar.” Ta bayyana.

A taron na kaddamar da shirin kwanaki uku an rarraba kayan tallafin rage radadin cutar Korona da taimakawa dalibai da kayan komawa makaranta da masu lalurar musamman an kuma tallafawa jama’a da na’ukan kayan abinci da suka hada da shinkafa, gero, dawa, masara, da man girki. Haka ma an rarraba tabarmi, turmi da tabarya, da injunan nika da teloli an kuma duba lafiyar al’umma tare da ba da magani kyauta.

Tun da farko Kwamishinar Ma’aikatar Jin Dadin Jama’a, Farfesa Ai’sha Madawaki Isa ta ta bayyana matar Gwamnan a matsayin gwarzuwar mace wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ci-gaban al’umma a karkashin Gidauniyarta.


Farfesa Sadiya Omar ta gabatar da kasida Akan ‘yan tarun Nana Asmau diyar Shehu Usman abin da ya kara jan hankalin mutane ga gudunmuwar ‘yan makarantar don a rika koyi da su a wurin gina al’umma mai basira.

Mai ba da shawara ga gidauniyar bangaren Sharia Barista Buhari Maigwandu ya bayyana yadda Asusun ke gudanar da Ayukkansu a wurin bin dokoki.


Dimbin wadanda suka amfana da tallafin sun yabawa Gidauniyar MMAWT kan namijin kokarin da take yi wajen kyautata jindadin da walwalarsu tare da rokon Allah ya saka mata da mafificin alheri ya kuma albarkace ta da maigidanta Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *