Spread the love

Tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa Honarabul Abdullahi Hassan ya yi alkawalin ba da tasa gudunmuwa ga wanda zai yi aikin unguwar Mabera in har gwamnatin jihar Sakkwato ta aminta a yi aikin gyaran magudanun ruwa da samar da sabbi don kawar da ambaliyar ruwa da suke fama da ita.

Abdullahi Hassan ya fitar da bayanin a turakarsa ta facebook ya ce “idan wanda ya yi alkawalin gyara Mabera ya tashi aiki zan ba da Tipa 100 na tsakuwa da aron mota tipa har a gama aiki amma ba da Mai ba da Injimin kwaba kankare da bayar da shawara kyauta in ana bukata.” a cewarsa.

Wannan wani yunkuri ne da ake bukata a rika ganin ‘yan siyasa na yi domin taimakon al’ummarsu da yankinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *