Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Don ganin cewa ta tabbatar da samun ingantaccen tsaro ga jama’arta, gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Bello Muhammed Matawallen Maradun, ta dauki nauyin horas da matasa 7500, aikin ‘yan sanda al’umma wanda gwamnatin tarayya Najeriya ta kirkiro.

Kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara Alhaji Suleiman Tunau Anka ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa rukuni na farko na matasan su 3,850, wadan da za su tashi daga hedikwar ‘yan sanda dake Gusau zuwa makarantun horas da ‘yan sanda dake jihohin Sokoto da Kaduna, bankwana.
Ya ce gwamna Bello Muhammed Matawalle ya dauki matakin daukar matasan su 7500 a duk fadin kanannan hukumomi 14 dake a jihar ta Zamfara domin a kara samun saukin yanda za’a magance matsalar rashin tsaro da kuma rage zaman kashe wando tsakanin matasan wannn jihar.


Kwamishinan ya kara da cewa gwamnati za ta dauki nauyin duk abinda suke da bukata daga nan gida har waje da za’a horas da su, har lokacin da suka kammala wata biyun da za su yi ana basu horon a makarantun ‘yan sanda.
Da yake nashi jawabi tun da farko, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Barrister Usman Nagogo ya ce shi wannan shirin na yan sandan al’umma , shiri ne wanda zai bada dama ga ‘yan kasa da suci gaba da kula da wuraren da suke zaune , kuma idan sunga bakuwar fuska sai suyi kokarin shaidawa jami’an ‘yan sanda domin daukar matakin daya kamata.
Nagogo ya bayyana cewa horon da za’a basu na wata biyu ne kacal, inda zasu fito da kayan yan sanda, yanda ba duk mutun zai gane cewa ba ainihin ‘yan sandan Najeriya ba ne. Kuma za’a tura su a kauyukan da suka fito, inda zasu aikin warware kananan matsaloli tsakanin al’ummarsu ba lallai sai an kawo ga ‘yan sanda ba.
“To kaga yanzu da wannan shirin na ‘yan sandan al’umma, ‘yan sandan Najeriya za su iya ba da karfi wajen magance manyan laifuka kamar da kuma aiki irin namu na ofis da dai makamantansu” inji shi.

Idan baku manta ba, a cikin watan ukku na wannan shekara Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Muhammed Adamu ya ce, bisa ga la’akari da yawan tashe tashen hankula da suka addabi kasar nan yasa dole ayi tunanin kirikira wannan hukuma ta yan sandan al’umma.

Yace game da yawaita kai hare haren yan bindiga, da garkuwa da mutane don amsar kudin fansa, fashi da makami a jihohin Kaduna, Niger, Kogi, Katsina da kuma Zamfara ya zama dole da mu fito da wannan tsari na yan sandan al’umma a fadin wannan kasar tamu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *