Spread the love

Jam’iyar APC mai mulki a Nijeriya ta ce za ta fitar da yanda tsarin babban taronta zai kasance a watan Nuwamba dake tafe.

Wata majiyar ce ta tsegunta wa manema labarai cewa jadawalin zai fito ne a watan Nuwamban nan.

Za a fitar da yanda yanayin taron zai kasance bayan an kammala zaben cike gurbi na wasu kujeru da hukumar zabe za ta gudanar a 31 ga watan nan.

Mataimakin Sakataren yada labarai na jam’iyar Yakini Nabena ya ce jam’iyar ta mayarda hankali kan zaben da ke tafe bayan nan za su sanarwa al’umma mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *