Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Rundunar sojan Najeriya dake yaki da ‘yan ta’adda da masu satar shanu da garkuwa da mutane arewa maso yamma cin Najeriya (Operations Sahel Sanity), tace ta aika da ‘yan ta’adda hudu lahira kuma ta kubutar da mutanen da ake garkuwa da su, a arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan bayani yana kunshe ne ga wata takardar bayani wanda sojoji suka fitar mai dauke dasa hannun mukaddashin daraktan hulda da kafafen yada labarai, Birgediya Janar Benard Onyeuku, aka rabawa yan jaridu a ranar talatar data gabata.

Yace zaratan sojojin sun samu nasarar kubutar da mutun shidda dake ga hannun su, bayan haka sojan sun kwato shanu 128, Awaki 6, Tumaki 18, da kuma bindiga kirar gida kwara biyu, da barayin shanu na jefar a yayin da suke gudun tsirar rayuwar su.

Birgediya Janar Benard ya kara da cewa sun kara kama wasu mutane ukku a karamar hukumar mulkin Musawa dake jihar Katsina, saboda ana tuhumar su da hannu dumu dumu cikin harkar garkuwa da mutane.

“Lokacin da mutanen mu na sintiri sun kama wasu mutane biyu wadanda ake zargi da tu’ammali da miyagun kwayoyi, da kuma karin wasu biya wadanda ke hada baki da ‘yanta’adda domin ba su bayanan sirri, an samu miyagun kwayoyi a hannunsu.

“Binciken farin da aka gudanar ya nuna cewa masu laifin suna da hannu cikin sayar da miyagun kwayoyi ga shugabannin ‘yan ta’adda kamar su Leko da sauran su.

“Wani mutun mai suna Umar Bello ya shiga komar mu, wanda ake tuhuma da yiwa barayin shanu safara kayan aiki, inda muka kamashi da Albarussai na musamman, da kayan surkulle na magani, da kuma buhun Gyada an harwa tsashi da Guro, da kuma buhu hudu na Gero, nuna tuhumar zai kai wayannan kayan ne a mabuyar yan ta’adda dake cikin daji.

” Da aka bincike shi, sai yace lalle ya taba kai kudin fansa amma sau daya kawai a dajin Madachi.

“Duk wadannan masu laifin da muka kama, zamu hannun taau ga hukumar data dace domin daukar matakin daya dace dasu, su kuma wadanda muka kubutar mun riga mun hannun ta su ga yan’uwansu”.inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *