Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya kubutar wasu yan Najeriya har mutane goma sha daya daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar zamfara ba tare da biyan kudin fansa ba.

Wannan nasarar tazo ne dai dai lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro, domin samar da hanya mafi sauki da za’a karin samun zaman lafiya ba tare da an zubar da jini ba.

Wayanda suka samu yancin su ga hannun yan ta’addar sun hada da maza takwas da mata ukku, dukanin su sun fito daga jihohin Bauchi, Niger, Sokoto da kuma Zamfara.

Mutanen da aka kubutar sun nuna farin cikin su ga gwamna bisa ga jajir cewar shi na ganin an samu cikakken tsaro, da kuma irin kokarin da yayi na ganin ansako su.

Gwamna Matawalle, wanda ya tarbe su a fadar gwamnati, ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa ba zata yi kasa a gwiwa ba, had sai ta tabbatar da an samu cikakken tsaro a fadin jihar ta zamfara.

Daga nan sai yabada umurnin a tafi dasu Assibiti domin a tabbatar cewa lafiyar su kalau, kafin a hannun tasu ga yan’uwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *