Spread the love

Babbar kotun Abuja ta nemi Sanata Elisha Abbo ya biya tarar kudi miliyan 50 kan zagin da yi wa mace mai sayar da kayan mata a Abuja.

Abbo dan jam’iyar PDP da yake wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattijai, na’ura ta dauko shi ya mammari Osimbira Warmarte a cikin shagonta a 11 ga watan mayun 2019.

Mai shari’a Samira Umar Bature a ranar Litinin ta yanke hukuncin Sanatan ya baiwa matar diyar miliyan 50 kan cin zarafinta da ya yi.

Sanatan bai karba waya ba a kiran da manema labarai suka yi masa kan jin ta bakinsa a tarar da aka yanke masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *