Majalisar matasa ta karrama Murtala Dan’iya da mukamin uban kungiya na Kasa

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.

An baiwa Shahararren mai taimakawa al’umma Alhaji Murtaka Abdulkadir (Dan’iyan Jarman Sokoto),  mukamin uban kungiyar majalisar Matasa ta kasa

 Shugaban kamfanin M- Square  integral motors Kaduna, ya samu zama cikin shugabannin Kungiyar na kasa, karramawar ta biyo bayan zaman da Ambassadors na jihohin Arewa maso yamma suka yi a jihar sokoto domin zabar Wanda zai shugabanci yankin a dattawan matasa.

Murtala Abdulkadir Dan Iya, ya samu wannan girmamawar ne a dalilin faifan bidiyo da hotuna da shaidun al’umma na wannan yankin Kan alherin da yake yi ga kungiyoyi, Marasa lafiya, tallafi ga mata na teloli, injimin sake-sake,  firizoji na kankara da ruwan sanyi, Abinci da magani a asibitoci, tallafin abinci ga gundomomin karkara da cikin birane, emergency patient, da taimakon matasa da alumma a lokacin Azumi da bukin sallah da gina masallatai da makarantu. Kungiyar ta yi fatan ya daure da ayukkan alheri da ya dauko don ba karamar nasara ba ce ga mutum ya zama cikin masu tausayin mabukata a cikin jama’arsa.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *