Spread the love

Daga, M.A Faruk.


Tsaro kalma ce da ke bayar da ma’anar kariya ga wasu gungun jama’a, ko unguwa ko gari ko yanki ko kasa baki daya domin tabbabatar da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. A kasar nan akwai hukumomin da alhakin sha’anin tsaro ya rataya a kan wuyansu kamar jami’an soja, ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya.
A zamanin da masu unguwanni da hakimai zuwa Gwamnati suna ba da muhimmanci sosai a fannin tsaron jama’arsu.

Sanin kowa ne irin kulawa da saka idanuwa ga duk wani bakon mutum ko gungun jama’ar da suka shigo unguwa ko cikin gari da sanin daga ina suke, me suka zo yi kuma yaya halayarsu take, da wadanne irin mutane suke hulda ta yadda a haka ne ake gane bata gari ko mutanen banza.


Tafiya na tafiya lokaci na canzawa a na samun wayewar kai, maimakon a ci-gaba da rike irin wannan halayyar sai aka yi watsi da ita har a ka kai wannan lokacin da unguwanni da garuruwanmu suka zama tamkar daji ba marufi, ko ina hanya ce wanda hakan ya sa sha’anin tsaro ya yi bahaguwar tabarbarewa. Idan muka yi duba a wannan zamanin da yanzu a ka samu yawaitar ababen  sadarwa da yawa kamar Radiyo, Talabijin, kafofin sadarwa yanar gizo, za mu ga cewa wasu daga cikinsu sun bada gudunmuwa a fannin magance matsalar tsaro wasu kuma akasin hakan.


A misali idan muka dauki fannin sadarwa a wayar hannu akwai kamfanoni guda hudu kamar MTN, 9Mobile, Glo da Airtel da muke amfani da su wajen sadarwa. A yanzu duk wani ko wasu bata gari suna amfani da waddannan layukan sadarwa domin awaitar da barna kamar zamba cikin aminci, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci. Irin sakaci da kamfunan sadarwa musamman na MTN ke yi wanda shi ne ya fi kamari wajen sayar da layi barkatai ya kara bada dama ga miyagun mutane wajen ci-gaba da cin karensu ba babbaka, dalilina a nan shi ne yawan tarin layukan da kamfanin MTN yake fitarwa ba tare da tabbatar da duk wanda zai yi amfani da shi ba yayi masa Rajista domin sanin mai layin ko shi wane ne daga ina yake domin za ka ga layuka a cikin unguwanni da kasuwa a na sayarwa da sunan layi mai Data da kuma kira a kan Naira Dari daya, wadannan layuka suna taimakawa masu ta’addanci ci-gaba da cin karensu ba babbaka.


Shawara a nan idan a na son dakile wannan matsala ta masu garkuwa da mutane, ko Aljannun Mutane ko ‘yan danfara to tabbas sai an takawa Kamfanin MTN burki kan sayar da layukan da ba su da ragista.

Don haka hukumomin tsaro da Hukumar Kula da Kamfunan Sadarwa ya kamata su dauki kwakkwaran matakin dakile wannan sakaci da Kamfanin MTN ke yi a kan lamarin tsaro a kasar nan.

Allah ya ba mu ikon gyarawa amin.

M. A Faruk Sokoto, 08098029098. (Mafaruk4u@yahoo.com)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *