Spread the love

Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce shi ba zai bayyana gaban kwamitin sauraren korafi da binciken almundahana da aka kafa domin dakataccen shugaban hukumar cin hanci da rashawa waton EFCC Ibrahim Magu.

Malami a bayanin da ya fitar wanda mai magana da yawunsa Dakta Umar Gwandu ya ce fadada gayyatar da kwamitin ya yi wadda ta shigo da ministan shari’a ya sabawa doka.

A cikin wannan watan ne ministan ya nuna cewa matukar kwamitin ya gayyace shi zai amsa gayyatar, sai ga shi a jiya(Alhamis) an yi gayyatar bai je ba don ba ta bisa doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *