Spread the love

“Dole ne gwamnatin tarayya ta mayar da tsohon farashin Man fetur da wutar lantarki” A cewar kungiyar Kwadago da ta kasuwanci.

Kungiyar kwadago a Nijeriya ta yi tsayin daka ba za ta ja ba ya ba kan yajin aiki da gudanar da zanga-zangar da ta shirya sai gwamnatin tarayya ta dawo da tsohon farashin man fetur da wutar lantarki da ta kakabawa mutane.

Manema labarai sun fitar da rahoton matsayar da kungiyar kwadago da kungiyar kasuwanci suka cimma a wurin zaman da suka yi da wakilan gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa.

Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnati wa’adin janye Karin farashin man fetur da wutar lantarki in ba ta aikata hakan ba za a ta shiga yahjin aikin gama gari.

Yajin aikin ana sa ran soma shi a ranar Litinin mai zuwa 28 ga watan Satumbar nan.

Kotun masana’antu ta dakatar da kungiyoyin ga yin kowane yajin aiki.

Alkali Ibrahim Galadima ne ya bayar da umarnin dakatarwar sai bayan an saurari maganar da aka shigar kan damar yin haka.

Galadima ya yi hakan ne a kan korafin da wasu kungiyoyi biyu suka shigar ta hanyar lauyansu Sanusi Musa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *