Spread the love

Shugaban Kwamitin amintattun jam’iyar PDP na kasa Sanata Walid Jibrin ya ce jam’iyar ta shirya samun nasara a zaben shugaban kasa da yin nasara a jihohin Nijeriya da kashi 90 a zaben 2023 dake tafe.

PDP ta fadi shugaban kasa a shekarar 2015 bayan shekara 16 suna mulki. 

Jam’iyar ta nuna ta dauko hanya mamaye jihohin Nijeriya da Kashi 90 matukar hukumar Zabe ta cigaba da gudanar da sahihin zabe a Nijeriya.

Saboda jam’iyar ta cimma bukatarta ta cigaba da sulhunta ‘yan jam’iyar saboda Kar a samu matsalolin nasarar zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *