Spread the love

Muhammad M. Nasir.

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci Ministan samar da wutar lantarki na Nijeriya Alhaji Saleh Mamman bayan gwamnatin jiha ta kasa cika alkawalin da ta yi wa Sakkwatawa na samar musu da wuta mallakar jiha waton(IPP).

Kafin gwamnatin Aminu Tambuwal ta fara a shekarar 2015, tsohuwar gwamnatin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ta zuba kudi biliyan 3.8 ga aikin da zimmar in an kammala shi za a samu wuta awa 24 a jihar Sakkwato har gwamnatin ta kare aikin bai kammalu ba.

Tambuwal ya yi alkawalin kammala aikin har ya kafa kwamiti da zimmar sanya wa aikin kudi sama da biliyan daya, gwamnatinsa ta kai matakin gwajin wutar sai aka ji lamarin ya yi tsit.

 Bayan kwashe sama da shekara 11 aikin ya lakume sama da biliyan hudu don samar da wuta mega wat 38, kawai an ji shiru sai a yanzu kuma gwamna ya ziyarci minista.

 A ziyarar Tambuwal ya nemi hadin kan gwamnatin tarayya na a  samar da wuta da hasken rana Mega wat 10 da zata iya hada kauyukka 100 a jihar, kamar yadda bayanin da mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai  Muhammad Bello ya fitar ga manema labarai a yau Talata.

Managarciya ta fahimci cewa sama da biliyan hudu da aikin ya lakume sun tafi kenan ba biyan bukata, ba kudi, hakan bai dace gwamnatin Tambuwal ba ta bari kudin al’umma su tafi hakan nan, ba wani gamsashen bayani da za a iya ji daga gwamnati. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *