Spread the love

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa wato INEC, ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayarsa na Jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Wannan ne karo na biyu da Obaseki ke doke Ize-Iyamu, inda a 2016 ma hakan ya faru, amma lokacin Obaseki na APC, Ize-Iyamu kuma PDP a can.

Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki ya samu ƙuri’u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 223,619.

Ɗan takarar Jam’iyyar SDP ya samu 323, sai kuma na Jam’iyyar LP ya samu 267.

Hukumar ta ce adadin masu waɗanda aka tantance domin kaɗa ƙuri’a shi ne 557,443, sai kuma adadin ƙuri’un da aka jefa 537,407.

Adadin ƙuri’un da aka jefa 550,242 sai kuma ƙuri’un da suka lalace a zaɓen 12,835.

‘Yan takara 14 ne suka kara a zaɓen wanda ya gudana a ranar Asabar, 19 ga watan Satumbar 2020.

Jihar na da rumfunan zaɓe 3,035 sannan akwai sama da mutum miliyan biyu da aka yi wa rajistar zaɓen, sai dai waɗanda suka jefa ƙuri’ar ba su wuce dubu 600 ba.

Zaɓen Edo dai kamar yadda masana siyasa suka bayyana, tamkar wani zakaran gwajin dafi ne tsakanin APC da PDP.

Wannan nasarar tana iya kawo karshen siyasar uban gida a jihar Edo, ganin duk ‘yan siyasar Nijeriya mutane ne masu son kansu da son cigaba da mulki ko bayan sauka da saman kujerar mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *