Spread the love

A jiya Alhamis wata mota da ake kyautata zaton Abensis ce ta fada gulbi ta nutse tare da wasu mutane a cikinta, tsawon kwana daya an kasa tsamo mutanen don rashin kayan aiki a wurin mahukuntan ba da agajin gaggawa.

Masunta ne ke ta kokarin gano in da motar take duk ba wata babbar mota da za ta iya fitar da mutanen.

Daraktan Hukumar Agajin ta jihar Sakkwato, Mustapha Umar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ana ci gaba da aikin gano mamatan da kuma ita motar.

“Ba mu san aihinin adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba, saboda ba mu samu wani ganau da yake a wajen yayin da lamarin ya auku ba.

“Sai dai gwanayen ninkayan da muka yi hayar su sun iya gano bagiren da motar take cikin kogin; inda suka shaida mana cewa karamar mota ce da za ta iya daukar mutum bakwai – ciki har da direba.

“Ko a yanzu da nake magana da kai, ana can ana ci gaba da gudanar da binciken gano gawarwakin kuma mun aika da janwe domin ciro motar daga cikin kogin”, inji shi.

Shi ma kakakin Hukumar Agaji ta Kasa, Aliyu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an hukumar sun dukufa domin aikin ceton

“Har sai mun iya tantance hakikanin wadanda suke cikin motar; sa’annan ne za mu iya fadin adadin wadanda suka mutu, saboda a tashar da motar ta tashi an tabbatar mana cewa babu wata motarsu da ta gamu da wani hadari a wannan ranar – hakan na nufin ita wannan motar ba ta taso daga wannan tashar ba ke nan”, inji shi.

Bayanai sun ce fasinjoji bakwai ne ke cikin motar da take kan hanyar zuwa Karamar Hukumar Illela, gabanin faruwar hatsarin.

Wata majiya ta ce motar ta kade wani mutum a kan babur wanda shi ma yana daga cikin wadan da suka salwanta.

Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ya biyo wurin ya tsaya ya nuna alhininsa ga lamarin ya yi addu’a ya wuce, har zuwa hada rahoton ba a samu ceto mutanen ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *