Spread the love


Haihuwar fari idan aka yiwa mace CS aka ciro jariri  sau daya toh akwai 75% chance na mace za ta iya haihuwa da kanta a ciki(juna biyu) na gaba. 


Sai dai wannan kwarin guiwar haihuwa da kanta a gaba yana da alaka da irin incision din da likitanta yayi wajen yanka mararta yayin CS din farko. Hakan yafi sauki ga wacce likita ya yi yankan a kwance wato daga gefen hagu zuwa dama (——-) abunda muke cewa VERTICAL maimakon wacce likitan ya yankata daga sama zuwa kasa ba…( | ) wato HORIZONTAL 


Bawai ina nufin wannan yankan na waje ba  da kuke iya gani da ido.. A’ah can jikin mahaifarta (uterus) incision din ciki nake nufi… domin yankan waje dama duk vertical ne (—-).


Sai dai yanayin da surgeon din da ya gani bayan ya yanka ya shiga shike sashi yin irin incision din da ya dace… ba za6a ake ba daka…sai dai in dama wanda ya yi quack ne ba aikinsa bane Kuma ba surgeon bane dan gyara samun sa’a ne toh har infection ma kila sai mace kaga ta samu ciwon yazo yai wahalar warkewa
Amma duk da haka indai mace tasan cs aka mata toh data sami ciki ya kamata mai gidanta yai tanadi da shirye shiryen kaita asibiti ta haihu.

Tunda komi na iya faruwa… kar azauna agida ajira naquda
Hakama wacce akai mata CS sau biyu tanada 50% chance na haihuwa da kanta amma dai da wahala…Amma inta mori lafiya kuma a CS din farko ya zamto bata sami complications na infection ba ta yadda raunin ya sami matsala ya jima bai warke ba kuma har ya rika ruwa…toh tana da greater chance na Natural birth akan wacce ta sami complications 
Amma in anyi CS 2 abaya yanzu haihuwa ta 3 ake tunkara toh zance ya qare ba zancen mace ta haihu da kanta… gwada hakan ka iya zama hatsari ma.

Sai dai avkasashen larabawa koma ince har anan din wasu matan masu sukuni bama su son Natural birth din… lafiyarsu kalau suke za6ar ai musu aiki aciro dan kurum basa son abunda zai bude su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *