Spread the love

Mahara sun shigo garin gidan Madi a karamar hukumar Tangaza dake jihar Sakkwato da daren jiya Laraba sun kashe ‘yan sanda biyu sun tafi da wasu matan aure uku da raunata daya.

Maharan da ake tsammanin sun kai 120 wasu kan babur wasu a kasa  sun yi wa garin kawanya tare da harbi kan mai uwa da wabi,  mutum daya ya samu rauni a garin.

Majiya ta ce mutanen sun shigo da dare  minti 40 suka yi  cikin gari, sun shigo daga kauyen Gurame da suka shigo garin sun aje motocinsu na yaki a wurare da dama kamar bakin masallacin juma’a na gidan sarki da hanyoyin shigowa cikin gari daga bayan gari.

Haka suka tafi ofishin ‘yan sanda sun yi musayar wuta tsakaninsu daga baya suka kashe DPO da Insfekta guda a wata mabuya da suka labe a bayan Injimin nika(markade), sun harbi daya a kafa.

Daga nan suka tafi gidan Alhaji Usman Shehu sun sace  matansa biyu, sun kuma tsaya a kauyen Gurame a gidan Alhaji Babangida shima sun tafi da matarsa daya kafin shiga dajin tsetse.

Jami’in hulda da jama’a ‘yan sanda ASP Muhammad A Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Karin bayani zai zo daga baya, in an kammala bincike.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *